Bababn Sakatare a ma'aikatar makamashi na kasar Godknows Igali ya sanar da hakan a wani taron kara ma juna sani a Abuja babban birnin tarayyar kasar,yana mai bayanin cewa Kasar na bukatar rungumar hanyar sadarwa ta zamani idan har tana son samun cigaba a bangaren makamashin ta da kuma kwarewa a ayyukan da sauran kasashen duniya.
Shi ma a na shi tsokacin a wajen taron Jakadan kasar Poland a Nigeria Prezamyslaw Niesiotowski ya shaida ma mahalarta taron da suka hada da 'yan asaslin kasar na Poland cewa kasar sa ta samu nasarar inganta tattalin arzikin ta ne ta amfani da hanyar sadarwa na zamani.(Fatimah Jibril)