Kafar yada labaru ta kasar Nigeria ta ba da labari cewa, firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa, kasar sa za ta tura rukunin kwararru wajen yaki da ta'addanci domin taimakawa kasar ta Nigeria wajen ceton 'yan matan nan daliban fiye da 200 da aka yi garkuwa da su a jihar Barno dake arewa maso gabashin kasar. (Amina)