Wata kungiyar masu gwagwarmaya da makamai a arewacin Najeriya mai suna Ansaru, ta sanar a ranar Asabar 9 ga wata cewa, ta kashe 'yan kasashen wajen nan bakwai, wadanda ta sace su cikin watan da ya gabata a jihar Bauchi.
Mutanen da aka yi garkuwar da su dai ma'aikata ne na wani kamfanin gine-gine mallakar 'yan kasar Lebanon, kuma kungiyar ta Ansaru ce ta sace su a ranar 17 ga watan Fabrairu.
Uku daga cikin mutanen 'yan Labanon ne, sauran hudun kuwa sun fito ne daga kasashen Burtaniya, da Girka, da Italiya, da kuma Philippines.
Ana dai zaton cewa kungiyar ta Ansaru, bangare ce ta kungiyar Boko Haram, wanda ke kunshe da masu tsattsauran ra'ayin Islama, wadda shawara tsakanin su da mahukuntan Nigeria kawo yanzu ta farkara.
Kwana daya kafin abkuwar lamarin, shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yi rangadi a jihohin Yobe, da Borno dake arewacin kasar, inda ya ce, ba za'a yafewa 'yan kungiyar ta Boko Haram ba, don ba'a san ko su waye ba.
Ya zuwa yanzu, gwamnatocin kasashen da abun ya shafa sun ce suna kokarin tabbatar da gaskiyar lamarin.
Daga shekara ta 2009 ya zuwa yanzu, matsalar tsaro na ci wa mazauna yankunan arewacin Najeriyar tuwo a kwarya, sakamakon hare-haren da magoya bayan kungiyoyin masu fafitikar suke kaiwa, lamarin da kuma ya janyo mutuwar mutane fiye da dubu 1.(Murtala)