Shugaban Najeriya ya mika sakon jaje ga kasar Sin bisa girgizar kasa da ta auku a wani yankin kasar
A ranar Asabar 20 ga watan nan ne shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya jajantawa takwaransa na kasar Sin Mr. Xi Jinping da raguwar al'ummar kasar ta Sin, don gane da girgizar kasa da karfinta ya kai mizani 7.0, wadda ta aukawa yankin gundumar Sichuan, dake kudu maso yammacin kasar, lamarin da ya haddasa rasuwar mutane fiye da dari 200, tare da jikkata wasu da dama, ya zuwa karfe 10 na ranar Lahadi ga wata.
Wata sanarwa da ta fito daga kakakin shugaban Najeriyar, Mr. Reuben Abati, ta bayyana jimamin shugaba Jonathan, wanda sanarwar ta ce ya bayyana matukar alhininsa ga iyalan wadanda wannan masifa ta aukawa. Har ila yau sanarwar ta bayyana goyon bayan da Najeriyar ke baiwa kasar Sin, don gane da aikin ceto, da ba da agaji da ake ci gaba da gudanarwa a wannan yanki da bala'in ya aukawa. (Saminu Alhassan)