Mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin watsa labaru Dr. Reuben Abati ya ce, a wannan lokaci da Mr. Kenyatta ke shirin kama aiki nan da 'yan kwanaki kadan, a matsayin sabon shugaban kasar ta Kenya, kuma shugaba na farko tun bayan da aka kaddamar da sabon kundin mulkin kasar, wato kundin dokokin da ya biyo bayan hatsaniyar da kasar ta fuskanta, jim kadan da kammalar babban zaben kasar na shekara ta 2007 da ya gabata, Mista Jonathan yayi kira gare shi, da ya zage damtse wajen farfado da ci gaban kasar ta Kenya, tare da aiwatar da sulhu tsakanin al'ummomi daban-daban.
Har wa yau kuma, shugaba Goodluck Jonathan yayi kira ga Kenyatta, da yayi namijin kokarin tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali, hadin-kai, da kuma neman samun ci gaba a kasar Kenya, ta yadda za'a biya bukatu, gami da gamsar da dukkanin jama'ar kasar, ciki har da abokan hamayya da kuma magoya-baya.