A cewar ministan, za'a kafa wannan cibiya kafin karshen wannan shekara, bayan bude cibiyoyin al'adun kasar a kasashen Brazil da Sin a shekarar 2008 da 2012.
Cibiyar za ta taimakawa wajen karfafa dangantakar al'adu tare da Afrika ta Kudu, har ma tare da sauran kasashen dake kuriyar Afrika, in ji mista Duke, tare da bayyana cewa wannan zabi an yi shi ne ta la'akari da rawar da Najeriya ta taka a cikin tarihin wadannan kasashen Afrika dake wannan shiyya. (Maman Ada)