Kwamitin tsaron MDD ya amince da kudurin daukar matakan soji a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya CAR. Kwamitin wanda ya baiwa tawagar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar AU wato MISCA damar kare rayukan fararen hula, ya ce, daukar wannan mataki ya zama wajibi, idan aka yi la'akari da yadda wannan kasa ke fuskantar hadarin fadawa mawuyacin hali na tashe-tsahen hankula marasa iyaka.
Kudurin daukar matakan soji wanda kasar Faransa ta gabatar, ya kuma ba da damar tura dakaru daga kasar ta Faransa, domin aikin kwantar da tarzoma a kasar Afirka ta Tsakiya, kasar da a baya Faransan ta taba mulka.
A wani ci gaban kuma babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya yi maraba da amincewar da kwamitin tsaron MDDr ya yi, da kudurin daukar matakan soji a Afirka ta Tsakiya, yana mai cewa, hakan zai ba da damar kashe wutar rikici dake ruruwa a wannan kasa.
Cikin sanarwar da kakakinsa ya fitar, Mr. Ban ya bayyana wannan kuduri a matsayin matakin da ya dace a dauka, wanda kuma ya zo kan lokaci.
Daukar matakin soji a wannan kasa da ta sha fama da rigingimu, ya biyo bayan barkewar tashe-tashen hankula a Bangui, babban birnin kasar tsakanin tsakanin tsoffin 'yan tawayen kasar da kuma dakaru dake goyon bayan tsohon shugaban kasar Francois Bozize. (Saminu)