Shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou ya kai wata ziyarar aiki a birnin Gao na kasar Mali a makon da ya gabata, inda ya samu ganawa da sojojin kasarsa dake cikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta kasa da kasa dake kasar Mali a karkashin jagorancin Afrika (MISMA).
Shugaban kasar Nijar ya kawo kwarin gwiwarsa da na al'ummar Nijar ga rundunar sojojin kasar dake yaki a kasar Mali. Kasar Nijar ta aika da babban rukuni dake kunshe da sojoji 650 da aka tura yankunan Gao, Menaka da Ansongo dake arewacin Mali. Shugaba Mahamadou Issoufou ya samu tarbo daga gwamnan yanki na Bakwai na kasar Mali, Mamadou Adama Diallo, sannan kuma ya samu gaisuwa da manyan jami'an soja da na fararen hula, wadanda a cikinsu akwai kwamanda na biyu na MISMA, 'dan kasar Nijar janar Seyni Garba.
Shugaban kasar Nijar ya nuna yabo na musammun ga ayyukan jarumtaka dare da rana da sojojin Nijar suke yi domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasar Mali. 'Kun samu shiga zukatan 'yan kasar Mali kuma kun samu yabo daga shugabannin kasarku, kasar Nijar na alfahari da ku domin bisa kokarinku ne kasar Nijar take girmama nauyin dake wuyanta.' in ji Mahamadou Issoufou, kafin ya kara kira ga sojojin kasar da su cigaba da matsa lamba da kokari domin murkushe 'yan ta'adda kwata-kwata daga arewacin kasar Mali. (Maman Ada)