Faraminstan kasar Afrika ta Tsakiya Nicolas Tiangaye ya ba da sanarwa a ranar Litinin a birnin Paris cewa, kasar Faransa za ta kara yawan sojojinta a kasar Afrika ta Tsakiya.
Za'a tura kimanin wasu karin sojoji 800 zuwa ga Afrika ta Tsakiya a tsakiyar watan Disamba domin taimakawa sojoji 410 da tuni suke a kasar, in ji kafofin watsa labarai na kasar Faransa. Hakan dai na daga cikin shirin kasar Faransa na kara yawan sojojinta a wannan kasa.
Kusan sojoji 800 za'a tura domin taimakawa sojoji 410 da a yanzu suke can in ji faraministan Afrika ta Tskiya Nicolas Tiangaye, bayan wata ganawarsa tare ministan harkokin wajen kasar Faransa Laurent Fabius a birnin Paris.
Duk wannan aiki, za'a yi shi ne a tsakiyar watan Disamba bayan amincewa da kudurin a kwamitin tsaro na MDD, in ji mista Tiangaye.
A nasa bangare, Faransa Laurent Fabius ya bayyana cewa, makasudin kasar Faransa shi ne domin tallafawa dakarun tawagar MDD a kasar Afrika ta Tsakiya MISCA a fannonin aikin soji, kayayyaki da kuma fasaha. (Maman Ada)