Rundunar sojojin kasar Afrika ta Kudu ta karyata a ranar Laraba wasu labarai dake nuna cewa, wasu sojojinta sun mutu ko suka ji rauni a kasar DRC-Congo. 'Wadannan labarai ya kamata a dube su a matsayin wata forfaganda kawai da yaki da hankalin mutane daga bangaren dakarun 'yan tawayen kasar DRC-Congo.' in ji kakakin rundunar sojojin tsaron kasar Afrika ta Kudu (SANDF), mista Xolani Mabanga a cikin wata sanarwa. Haka kuma ya bayyana cewa, 'yan tawayen kasar Congo suna kokarin fifita nasarar da ba gaskiya da suka ce sun samu kan dakarun wanzar da zaman lafiya. Mista Mabanga ya tabbatar da cewa, an samu wani artabo tsakanin sojojin majalisar dinkin duniya da 'yan tawaye a ranar Asabar. A yayin wannan fiti na fito, wata roka ta fado kusa da wani sansani inda aka jibge sojojin wanzar da zaman lafiya na kasar Afrika ta Kudu da Tanzaniya dake cikin tawagar MDD, in ji mista Mabanga, inda ya kara da cewa, tarwatsewar wannan nakiya ta dan janyo raunin wani sojin Afrika ta Kudu da wasu sojojin Tanzaniya biyu. (Maman Ada)