Shugaba Xi wanda shine shugaban kwamitin sojan kasar ya shaida ma dakarun kasar a lokacin da yake duba cibiyar rundunar sojin saman kasar cewa su gaggauta ayyukan fasaha a bangaren ilimin sararin samaniya su kuma zurfafa matakan kai hari da kuma kare kansu.
A lokacin ziyarar Shugaban yace kada a yi sanyi a gwiwwa wajen kokarin da ake yi na neman jirgin saman Malaysiya da ya bace,a lokacin da yake jawabi ta hoton bodiyo ga sojojin saman dake gudanar da wannan aikin na neman jirgin. (Fatimah Jibril)