in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Faransa za ta rage sojojinta da ke Mali
2014-01-09 10:07:33 cri

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya bayyana cewa, a tsakiyar watan Fabrairu, kasarsa za ta rage yawan sojojinta da ta tura zuwa kasar Mali dake yammacin Afirka daga 2,500 zuwa 1,600.

Shugaban ya bayyana hakan ne ranar Laraba cikin jawabinsa na sabuwar shekara ga dakarun kasar, inda ya ce, ya zuwa karshen shekara, kasar za ta kara rage yawan sojojinta zuwa 1,000. Adadin da shugaban ya ce, zai iya tunkarar duk wata barazana da ka iya kunno kai, ganin cewa har yanzu akwai kungiyoyin 'yan ta'adda a arewacin kasar ta Mali.

A shekarar da ta gabata ce, kasar ta Faransa ta kaddamar da hare-hare ta sama da ta kasa bisa bukatar hukumomin kasar ta Mali da nufin taimaka mata ta fatattaki 'yan tawayen da suka mamaye arewacin kasar.

Shugaba Holande ya kuma yi alkawacin cewa, za a damkawa dakarun Afirka da na MDD ikon kula da harkokin tsaron kasar ta Mali da zarar sojojin Faransa sun kammala aikinsu, (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China