in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rukuni na biyu na sojojin kasar Congo ya isa Bangui na CAR
2013-09-16 12:39:54 cri

Wata tawagar dake kunshe da sojoji 200 na rundunar sojojin kasar Congo (FAC) ta tashi a ranar Lahadi zuwa Bangui, babban birnin kasar Afrika ta Tsakiya (CAR), inda za ta shiga cikin tawagar tabbatar da zaman lafiya a tsakiyar nahiyar Afrika (MICOPAX), tare da sojojin mambobin gamayyar tattalin arzikin kasashen dake tsakiyar Afrika (CEEAC). Tawagar MICOPAX, za'a maida ita wata tawagar kungiyar tarayyar Afrika AU. Kafin tashin wadannan sojoji na Congo, shugaban rundunar sojojin FAC, janar Guy Blanchard Okoi ya bukaci sojojinsa da su kiyaye mutuncinsu da kuma dokokin kasar Afrika ta Tsakiya. 'Gwamnati ta kebe muku kayayyaki da kudade, ta yadda za ku iyar gudanar da wannan aiki yadda ya kamata, dalilin haka ne muke dogaro da ku domin ku ba da misali mai kyau, musamman a bangaren kwarewa, bin sharudan aiki, hadin kai da kuma bin doka.' in ji janar Blanchard Okoi.

Wannan rukuni na biyu na kasar Congo ya tashi zuwa birnin na Bangui da motocin yaki da na jigilar sojoji a karkashin jagorancin kaftan Ange Wilfried Aboni Angoya, sojojin da za su iske wasu 150 da suka bar Brazzaville tun ranar 27 ga watan Julin da ya gabata.

Shugabannin kasashen CEEAC sun dauki niyya a wannan shekara na kara yawan sojojin tawagar MICOPAX zuwa sojoji dubu biyu domin taimakawa tawagar wannan shiyya cika aikinsu na tabbatar da zaman lafiya a kasar Afrika ta Tsakiya (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China