Gwamnatin kasar Burundi tana shirin tura sojojinta zuwa kasar Mali da kasar Afrika ta Tsakiya a cikin tsarin aikin tawagogin tabbatar da zaman lafiya, in ji shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza a ranar Litinin a cikin wani jawabinsa zuwa ga 'yan kasa na cikin shekara uku na wa'adin mulkinsa.
Mista Nkurunziza ya bayyana kwarewar kasar Burundi a kan fagen daga, wadda tuni ta taimaka a cikin tawagogin wanzar da zaman lafiya da dama a cikin kasashen da suka yi fama da yaki, kamar su Somaliya, Sudan, Cote d'Ivoire da Haiti, tare kuma da samun yabo daga kasashen duniya.
Haka kuma shugaba Nkurunziza ya ba da sanarwar cewa, kasar Burundi nan ba da jima ba za ta tura 'yan sanda a cikin irin wannan tawaga.
A cewar Nkurunziza, dalilin magance matsalar tsaro a dukkan fadin kasar Burundi, ya sanya gamayyar kasa da kasa ta ba da yardarta ga kasar Burundi, da kuma neman kwarewarta a cikin irin wadannan ayyuka na tabbatar da zaman lafiya a cikin kasashen dake cikin yaki. (Maman Ada)