Shugaba Francois Hollande na kasar Faransa ya ce, dakarun kasarsa za su fara daukar matakan soji a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya CAR ba tare da wani bata lokaci ba.
Shugaba Hollande ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis, yana mai cewa, daukar wannan mataki ya zama wajibi, duba da yadda tashe-tashen hankula ke dada ta'azzara a Bangui, babban birnin kasar.
Ya ce, an yi kira da Faransa da ta dauki matakan dakile aukawar al'ummar kasar Afirka ta Tsakiya cikin mummunan halin ni-'ya-su, don haka dakarun kasarsa za su rungumi wannan aiki ba tare da wani jinkiri ba.
Tuni dai mahukuntan kasar Faransan suka tura dakarun soji 600 zuwa birnin na Bangui, domin ba da kariya ga 'yan Faransa dake can, da ma ragowar fararen hula, yayin da ake kuma sa ran linkawar wannan adadi nan da 'yan kwanaki masu zuwa. (Saminu)