in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Uganda ta ki amince da janye sojojinta daga Sudan ta Kudu duk da kirar Amurka
2014-02-12 11:01:01 cri

Kasar Uganda ta bayyana a ranar Talata duk da matsin lamba daga kasashen duniya cewa, ba za ta janye sojojinta ba daga kasar Sudan ta Kudu makwabciyar kasarta. Mista Henry Okello Oryem, ministan kasa da harkokin wajen Uganda ya shaida wa 'yan jarida a birnin Kampala cewa, kasar Uganda ba za ta damu da kirarAmurka game da janye sojoji daga kasar Sudan ta Kudu har sai kasar ta samu zaman lafiya.

Babu wata kasar da za ta iya tilasta ko baiwa Uganda wani umurni, in ji mista Henry Okello Oryem.

A makon da ya gabata, kasar Amurka ta bukaci ficewar dukkan sojojin kasashen waje dake kasar Sudan ta Kudu, domin taimaka sasanta rikicin zubar da jini tsakanin sojojin shugaba Salva Kiir da dakarun dake biyayya ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Riek Machar.

Duk da cewa, sanarwar ba ta ambata kasar Uganda kai tsaye ba, amma sojojin Uganda ne na dafawa sojojin gwamnatin Sudan ta Kudu domin fatattakar 'yan tawaye.

Laftanan kanal Paddy Ankunda, kakakin rundunar sojojin Uganda ya bayyana cewa, sojojin kasar za su cigaba da tsayawa a Sudan ta Kudu domin ganin an kawo karshen tashe-tashen hankali a Juba da sauran yankunan kasar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China