in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin MDD a Guinee-Bissau ya zargi wasu jam'iyyun siyasar kasar da mallakar sojojin sa kai
2013-12-04 10:56:21 cri

Manzon musamman na sakatare janar na MDD dake kasar Guinee-Bissau, Jose Ramos Horta ya zargi wasu jam'iyyun siyasa da mallakar sojojin sa kai.

Akwai jam'iyyun siyasa na kasar dake da sojojin sa kai. Wannan ba abu ba ne da za'a iyar amincewa da shi a cikin wata kasar da ta samu wayewar kai kamar Guinee-Bissau, in ji wannan jami'i a gaban manema labarai a kwanan nan.

Mista Horta ya bukaci wadannan jam'iyyun siyasa da su karbe makaman dake hannun sojojin sa kan nasu. Ya fi kyau wadannan jam'iyyun siyasa da kansu musammun ma shugabannin sojojin da suka yi juyin mulkin ranar 12 ga watan Afrilun shekarar 2012, su karbe makamai daga wadannan mutane, in ji wannan jami'i da ya taba samun kyautar Nobel ta zaman lafiya.

Haka zalika mista Ramos Horta ya yi allawadai da sojojin Guinee-Bissa cewa, ya kamata rundunar sojojin kasar ta bar yin shisshigi a cikin harkokin siyasa da kuma yin barazana ga fararen hula.

A tsawon shekaru 15 da suka gabata, Guinee-Bissau ta rika fama da shisshigin sojojin kasar a cikin harkokin siyasa na wannan kasa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China