An ba da labari cewa, ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ta sanar a ran 7 ga wata cewa, Iran za ta yi shawarwari kai tsaye da Amurka da Rasha kan batun nukiliyarta, sannan, za ta tattauna da sauran bangarorin da batun ya shafa gaba da gaba
Game da wannan batu, Madam Hua ta bayyana wa manema labaru a wannan rana cewa, tun farkon wannan shekara da muke ciki, kasashe shida da wannan batu ya shafa sun riga sun sulhunta a dukkan fannoni da Iran sau hudu, yanzu za a yi sabon zagaye na tattunawa daga ran 16 zuwa 20 ga wannan watan. Yayin da ake fuskantar tafiyar hawainiya wajen yin shawarwarin, abubuwa dake gaban bangarorin daban-daban za su kara wuya, abin da ya sa ake bukatar bangarorin daban-daban da su kawar da bambancin ra'ayi dake tsakaninsui. A ganin Sin, yadda kasashen 6 suke kokarin musayar ra'ayi da bangaren Iran zai taimakawa samun fahimtar juna tsakaninsu, da ciyar da aikin shawarwarin gaba.(Amina)