Abbas Aragchi ya shedawa manema labaru cewa, saboda bambancin ra'ayi sosai kan wasu batutuwa tsakanin bangarorin daban-daban, ba a cimma matsaya daya wajen tsai da daftarin ba tukuna, hakan ya bayyana cewa, babu wata nasarar da aka samu a taron. Saidai mista Aragchi bai fayyace irin bambancin ra'ayi sukan da ake fuskantaci ba. Haka kuma jami'in na Iran ya bayyana cewa za a ci gaba da shawarwarin, inda bangarorin daban-daban za su ci gaba da shawarwari a wani sabon zagaye a watan Yuni. Bangarori daban-dabann da batun ya shafa kuma, na fatan za ahar yanzu suna da damar cimma wata yarjejeniya a dukkan fannoni kafin wa'adi na matakin farko da taron Geneva ya tsayar kan batun nukiliyar Iran ya cika, wato kafin ran 20 ga watan Yuli.
Bisa matsayin da bangarorin daban-daban da wannan batu ya shafa suka bayar a kwanakin baya, a cikin shawarwarin wannan zagaye da aka fara a ran 14 ga wata, bangarorin daban-daban na shirin cimma yarjejeniya a dukkan fannoni kan batun nukiliya da zummar kwantar da hankula bangarori daban-daban kan shirin nukilya na kasar ta Iran da janyo janye takunkumin da aka garkamawa Iran. (Amina)