Araqchi ya ce an shirya gudanar da wannan taro ne a birnin New York na kasar Amurka, inda ake sa ran musayar ra'ayi, da ci gaba da aiwatar da shawarwari kan harkokin da suka shafi fasahohin nukiliyar kasar ta Iran, da nufin kammala karshen daftarin yarjejeniyar da ta shafi hakan, ko da yake bai yi wani karin haske game da hakan ba.
Yayin taron shawarwarin da aka kammala a birnin Vienna a makon da ya gabata dai, bangarorin da wannan batu ya shafa sun cimma matsaya guda, kan batun ci gaba da shawarwarin da ake yi.
Bugu da kari, baya ga taron shawarwari tsakanin wakilan kasashe masu ruwa da tsaki kan batun nukiliyar kasar ta Iran, da takwarorinsu na gwamnatin Iran din, za a kuma gudanar da wani taron shawarwarin na daban, tsakanin kasar Iran da kasashen shida a birnin New York a ranar 13 ga watan Mayu, taron da ake fatan zai ba da damar tattaunawa kan yadda za a tsara karshen daftarin yarjejeniya dangane da batun nukiliyar kasar Iran. (Maryam)