Kasashe shida da batun nukiliyar kasar ta Iran ya shafa wato Amurka, Birtaniya, Faransa, Rasha, Sin da Jamus sun yi shawarwari zagaye na hudu da kasar Iran a ran 14 ga wata a birnin Vienna, bangarorin biyu kuma sun fara tsai da daftarin yarjejeniyar warware batun nukiliyar kasar ta Iran a dukkan fannoni. (Amina)