in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran ta yi alkawarin ci gaba da shirin ta na Nukiliya
2014-03-16 16:17:25 cri
Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Zarif, ya ce kasar sa ba ta da niyar yin watsi da dukkanin shirye shiryen ta na Nukiliya, duba da cewa shirin kasar game da makamashin ya kebanci ayyukan amfanin farar hula ne kadai.

Zarif ya bayyana hakan ne a jiya Asabar, gabanin babban taron tattaunawa da wakilan kasar za su fara, da masu ruwa da tsaki na manyan kasashen duniya.

Bugu da kari ministan wajen kasar ta Iran, ya yi kira ga Amurka, da ta fuskanci hakikanin gaskiya, ta kuma dauki matakin da ya dace, dangane da batun Nukilyar kasar ta Iran, matakin da acewar sa zai kawo karshen gutsiri-tsomar da ake ta faman yi kan batun.

Wannan dai tsakoci na Zarif tamkar mai da martani ne, ga kalaman da sakataren wajen Amurka John Kerry ya yi a ranar Alhamis din da ta gabata, in da ya ce dole ne Iran ta kuduri aniyar rungumar wata matsaya mai wuya, domin kawo karshen wannan batu na Nukiliyar ta. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China