in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran za ta yi shawarwari da Amurka da Rasha kan batun nukiliyar kasar
2014-06-08 16:55:07 cri
Kafofin yada labaran kasar Iran sun bayyana shirin mahukuntan kasar ta Iran game da gudanar da shawarwari tsakanin su da kasashen Amurka da Rasha kan batun nukiliyar kasar.

Kaza lika kamfanin dillancin labarun Iran na IRNA, ya rawaito ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Iran na cewa, daga ranar 9 zuwa 10 ga watan nan da muke ciki, wakilan kasar za su yi shawarwarin da mataimakan ministoci da wakilan Amurka a Geneva, kafin daga bisani su zanta da wakilan Rasha tsakanin ranekun 11 zuwa 12 ga wata a birnin Rome.

Bugu da kari an bayyana cewa, mahukuntan na Iran na da burin ganawa da wakilan kasahe shida da batun Nukiliyar ta ya shafa kafin ranar 16 ga wata a birnin Vienna. Tattaunawar da za ta biyo bayan wacce za ta yi, za ta gudanar tare da wakilan kasashen daban daban banda Amurka da Rasha.

Dadin dadawa, majalisar gudanarwar Amurka ta tabbatar da za a gudanar da wasu shawarwari tsakaninta da Iran, ganawar da ta kunshi zaunannen mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka William Burns, da mataimakin sakataren harkokin wajen kasar mai kulawa da harkokin siyasa, Wendy Sherman.

Inda bangarorin biyu suka amince da aiwatar da kudurorin dake kunshe cikin shawarar da aka cimmaIran da kasashen shida da batun nukiliyar kasar ya shafa sun cimma matsaya daya a Geneva cikin watan Nuwamban bara.

Bisa wannan shiri dai an amince Iran ta dakatar da wasu ayyukan sarrafa makamashin nukiliyar ta cikin tsawon watanni shida, ta yadda hakan zai kai ga dakatar da takunkumi da kasashen yammacin duniya ke kakaba ma ta a fannin tattalin arziki.

A daya bangaren kuma, Iran da kasashen shida za su yi shawarwari kan yarjejeniyar karshe game da daidaita batun nukiliya a dukkanin fannoni, a kokarin neman samun wata hanyar warware wannan matsala cikin dogon lokaci.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China