Amano wanda ya bayyana hakan yayin wani taron manema labaru, ya ce hukumar ta IAEA na yin hadin gwiwa da kasar Iran, domin tantance halin da ake ciki game da batun nukiliyar kasar, koda yake lokaci bai yi ba, na gabatar da ra'ayin hukumar game da aikin da ake gudanarwa.
A baya bayan nan wani rahoto da Amano ya gabatar ga majalisar hukumar ta IAEA ya bayyana cewa, kasar Iran ta na hakikanin hadin gwiwa tare da hukumar, lamarin da ya nuna cewa, Iran din na bayani ga hukumar game da batun aikin soji a karo na farko.
Kaza lika yayin taron manema labaru da aka gudanar a yayin taron hukumar na jiya Litinin, Amano ya bayyana cewa, yanzu dai babu wani jadawali na warware matsaloli da ake fuskanta, a shirin nukuliyar kasar ta Iran. Don hakan ta dace IAEA ta kara yin hadin gwiwa da kasar ta Iran, wajen aikin bincike game da abubuwan da Iran din ta gabatar game da shirinta na nukuliya, ta yadda hukumar za ta kara sanin shirin da ya dace a yi a dukkan fannoni. (Zainab)