Shugaban addini na kasar Iran Ali Khamenei ya bayyana a ran 9 ga wata cewa, Iran ba za ta daina shirinta na makamashin nukiliya ba, ya bukaci masu nazari na kasar su ci gaba da gudanar da bincike kan fasahohin makamashin nukiliya bisa tsarin 'yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya'.
Ranar 9 ga wata, rana ce ta fasahar makamashin nukiliya a kasar Iran, a wannan rana kuma, shugaban addini na kasar Iran Ali Khamenei ya gana da jami'an hukumar makamashin nukiliya ta kasar Iran, da wasu kwararru a wannan fanni.
Khamenei ya yi nuni cewa, ko da yake ana iya amfani da fasahohin nukiliya a fannoni da dama, amma ga kasar Iran, karfafa imanin kasar da dasa tushe ga sauran fasahohi, sun zama sakamakon da ya fi muhimmanci wajen raya fasahohin nukiliya da Iran take gudanarwa. (Danladi)