Wani jami'in hukumar makamashin nukiliyar kasar Iran ya bayyana a ran 20 ga wata cewa, Iran ta riga ta kammala aikinta na saukaka ingancin sinadarin Uranium da aka tace kashi 20 bisa darin sa. Wannan aiki dai na cikin sharuddan yarjejeniyar wa'adin farko, kan matsalar nukiliyar kasar da aka daddale.
Kakakin hukumar makamashin nukiliyar kasar ta Iran Behrouz Kamalvandi ya bayyana cewa, bisa yarjejeniyar, an bukaci Iran ta saukaka rabin ingantaccen sinadarin Uranium da take da shi, da aka tace kashi 20 bisa dari na sa, wanda adadin nauyinsa ya kai kilogiram 209. Wato Iran ta saukaka kilo 104.5 daga cikinsa, ta yadda zai zama mai kunshe da ingancin kasha da kashi 5 bisa dari. Ya ce, a halin yanzu, Iran ta riga ta gama wannan aiki.
Behrouz Kamalvandi ya kara da cewa, a cikin watanni 3 masu zuwa, Iran za ta mayar da sauran rabin sinadarin Uranium zuwa Uranium oxide, domin kawo karshen dukkan ayyukan da aka tanada a cikin yarjejeniyar wa'adin farko, kan matsalar nukiliyar ta Iran da aka daddale. (Danladi)