Kakakin majalisar gudanarwa ta kasar Amurka Jen Psaki ta bayyana a ran 15 ga wata cewa, bisa ga rawar da sabon wakilin Iran da ke MDD Hamid Aboutalebi ya taka a rikicin garkuwar jama'a a shekara ta 1979, Amurka tana tsayawa tsayin daka cewa, ba za ta bayar da takardar Visa gare shi ba.
Iran ta kai kara ga MDD a ran 15 ga wata, ta ce, za ta daukaka takarar kara bisa ajandar dokoki, amma ba za ta canza zaunannen wakilinta a MDD ba.
Kakakin babban sakataren MDD Stephane Dujarric ya tabbatar da cewa, za a kira taro don tattaunawa kan wannan lamari. (Danladi)