Ranar 8 ga wata, za a yi shawarwari kan batun nukiliyar kasar Iran na sabon zagaye a birnin Vienna. A gabannin farawar shawarwarin, Abbas Araqchi, mataimakin ministan harkokin wajen Iran kuma mataimakin wakilin kasar mai kula da harkokin shawarwarin ya bayyana a ranar 6 ga wata cewa, Iran na fatan bangarorin da za su shiga shawarwarin za su kara kawar da sabanin da ke tsakaninsu, da kuma cimma daidaito kan wasu muhimman batutuwa, ta yadda za su iya fara tattaunawa kan wasu batutuwa filla-filla tare da soma tsara shirin yarjejeniyar karshe.
Mista Araqchi ya kara da cewa, watakila za a soma tsara shirin yarjejeniyar bayan tsakiyar watan nan. (Tasallah)