'Yan majalissar da suka gabatar da kudurin sun ce sabon jakadan kasar ta Iran ya cancanci wannan mataki, kasancewarsa daya daga dakarun da suka yi garkuwa da Amurkawa 52, yayin da kungiyarsu ta kame ofishin jakadancin Amurkan dake birnin Tehran a shekarar 1979.
Tuni dai aka mika wannan kudurin doka ga fadar shugaban kasar ta Amurka domin tabbatarwa.
Da ma dai fadar ta White House ta bayyanawa mahukuntan kasar ta Iran rashin gamsuwarta da zaben Aboutalebi a matsayin jakadanta, ko da yake kakakin fadar ta White House Jay Carney bai bayyana ko shugaba Obama zai amince da kudurin ba.
Sai dai ya ce lamarin ba zai shafi tattaunawar da ake yi game da nukiliyar kasar ta Iran ba. Tattaunawar da a cewarsa take tattare da karin nasarori.
A nata bangare kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Marzieh Afkham, ta ce matsayin da Amurka ta dauka don gane da wannan batu abu ne da sam ba za a amince da shi ba.
MDD da kasashen Amurka, da Birtaniya da Sin ne ke tattaunawa da kasar ta Iran game da hanyoyin warware takaddamar dake tattare da nukiliyarta. Sauran kasashen dake cikin wannan shiri sun hada da Faransa, da Rasha da Jamus. (Saminu Hassan)