Bisa kudurin farko, kwamitin ya kara wa'adin aikin kungiyar ba da taimako dake Somalia zuwa watanni 12, domin ta ci gaba da gudanar da aikin shiga tsakani a kasar, da goyon bayan yunkurin gwamnatin kasar na shimfida zaman lafiya da zaman jituwa a kasar, da ba da shawarwari kan yadda za a iyar tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwar kasar, da ba da taimako wajen kyautata ayyukan gwamantin kasar, gami da bincike da ba da rahoto kan yanayin hakkin dan Adam na kasar.
Sa'an nan game da kuduri na biyu, kwamitin ya kara wa'adin aikin ofishin kiyaye zaman lafiyar dake Guinea Bissau zuwa watanni 6. Haka kwamitin ya yi maraba da nasarorin da kasar Guinea Bissau ta samu wajen gudanar da babban zabe da zaben majalisar dokokin kasar, inda yana ganin cewa, ya kamata ofishin ya ba da taimako wajen farfadowar wannan kasa a fannoni daban daban, kiyaye tsarin mulkin kasar, da kara azama ga yin shawarwari a duk fadin kasar bayan zaben. Bugu da kari, an kuma jaddada cewa, ya kamata a kira wani taron kasa da kasa kan ba da taimakon kudi don tallafa wa kasar Guinea Bissau samun farfadowa cikin sauri. (Maryam)