Fadar shugaban kasar Guinea Bissau ta ba da sanarwa a ran 28 ga wata cewa, kasar za ta gudanar da zaben shugaban kasar da na majalisa a ran 24 ga watan Nuwamba na bana.
Sanarwar ta nuna cewa, bayan tattaunawa tsakanin shugaban rikon kwarya da jam'iyyu da kungiyoyi daban-daban na kasar, daga baya, shugaban ya tabbatar da lokacin yin zabe. Ban da haka, sanarwar ta ce, hukumar zabe ta kasar ta tabbatar da cewa, akwai sharadi mai kyau wajen yin zabe a watan Nuwamba mai zuwa.
An ba da labari cewa, a ran 12 ga watan Afrilu na shekarar bara, an yi juyin mulkin soja a kasar, inda aka hambarar da gwamnati karkashin jagorancin jam'iyyar PAIGC. A watan Mayu na shekarar 2012, Guinea Bissau ta kafa gwamnatin wucin gadi bisa matsin lambar kasa da kasa. Za a kawo karshen gwamnatin wuci gadin ne domin tabbatar da lokacin yin sabon zabe, ta yadda za a farfado da zaman oda da doka a kasar. (Amina)