Ana dai sa ran 'yan kasar su kimanin 775,000 ne zasu kada kuri'un su, yayin zaben na shugaban kasar, da 'yan majalissun dokoki.
Akwai dai 'yan takara 13 dake neman kujerar shugabancin kasar, yayin da kuma jam'iyyu 15 suka fidda 'yan takarar neman kujerun majalisun dokoki.
Cikin manyan 'yan takarar kujerar jagorancin kasar akwai tsohon ministan kudin kasar Jose Mario Vaz na jam'iyyar PAIGC, da Abel Lamedi Incada, da kuma Paulo Gomes. (Saminu Alhassan)