Yayin ganawarsa da 'yan jaridu bayan saukarsa, shugaba Nhamadjo yace yana kara samun sauki, a lokaci guda kuma yana ci gaba da sham magani.
Shugaban dai ya koma gida ne, dai dai lokacin da al'amura ke ci gaba da tsananta a kasar, musamman ganin yadda tuni aka kame tsohon kwamandan sojin ruwan kasar Bubo Na Tchuto, tare da zargin wasu jami'an gwamnati, da kuma wasu manyan jiga-jigan rundunar sojin kasar, da hannu cikin harkokin da suka shafi fataucin miyagun kwayoyi, da kuma hada kai da kungiyoyin 'yan ta'adda na kasar kwalambiya, a hada-hadar cinikayyar makamai ba bisa ka'ida ba.
An ce dai wasu daga jami'an da sashen yaki da muggan kwayoyi na kasar Amurka ya cafke, sun ambaci sunan shugaba Nhamadjo, da firaminista Rui Duarte Barros, cikin wadanda ke da hannu a waccan haramtacciyar sana'a. ko da yake dai tuni shugaban kasar ya yi watsi da wannan zargi, yana mai cewa suka ne kawai, na masu mugun nufi.
Shugaba Nhamadjo dai ya bar kasarsa tun ranar 20 ga watan Maris daya gabata, inda da fari ya sauka birnin Abidjan na kasar Cote d'Ivoire, domin fayyace shirin mika mulkin kasar tasa ga zababbiyar gwamnati, kafin daga bisani ya wuce kasar Jamus, inda aka binciki lafiyarsa. A wannan tsakani ne aka damke Mr. Na Tchuto, bisa zargin aikata laifuka masu alaka da fataucin kwayoyi. Baya ga shi Mr. Tchuto, ofishin mai gabatar da kara na kasar Amurka, ya bada sammacin kame babban hafsan rundunar sojin kasar Antonio Injai, bisa zargin sa da aikata laifukan da suka danganci fataucin kwayoyi da kuma cinikayyar makamai ga 'yan tawayen kasar kwalambiya. (Saminu Alhassan)