in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Somaliya da tawagar AMISOM sun yi alla wadai da tagwayen hare hare a birnin Mogadishu
2013-09-08 16:27:39 cri
Gwamnatin kasar Somaliya da tawagar wanzar da zaman lafita ta tarayyar Afrika dake kasar Somaliya (AMISOM) sun yi babbar suka tare da yin alla wadai kan wasu tagwayen hare hare da suka faru a ranar Asabar kan wani gidan cin abinci na jama'a dake birnin Mogadishu. Wata mota da aka dana bom ta tarwatse a ranar Asabar kusa da wani gidan cin abinci dake kusa da dandalin wasannin kwaikwayo, lamarin da ya yi sanadiyyar mutane goma sha takwas tare da raunana wasu kusan goma. Mintoci kalilan bayan wannan, wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa kansa a cikin wani gungun mutane dake kokarin zuwa inda bom ta farko ta tashi. Ministar harkokin wajen kasar Somaliya Fawzia Yusuf ta yi alla wadai da wadannan hare hare tare da kimanta su a matsayin wasu munanan ayyukan mai da hannun agogo baya kan kokarin da gwamnatin kasar take na tabbatar da zaman lafiya. Muna tir da alla wadai da babbar murya kan wadannan hare haren ta'adanci dake shafar fararen hula, in ji madam Yusuf.

A nasa bangare shugaban tawagar AMISOM, mista Mahmat Saleh Annadif shi ma ya yi tir da alla wadai da wadannan tagwayen hare hare, tare da bayyana cewa wannan wata manufa ce ta jinkirta ci gaban kasar Somaliya.

Tawagar AMISON za ta ci gaba da tallafawa kokarin jama'ar Somaliya wajen sake gina kasarsu, in ji shugaban tawagar AMISOM. Tuni dai kungiyar 'yan kishin Islama ta Al-Shebab ta dauki alhakin kai wadannan tagwayen hare hare na Mogadishu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China