Taron dake gudana a birnin Brussel ya shafi bullo da "sabbin manufofi kan kasar Somalia" bisa hadin gwiwar gwamnatin kasar Somalia da kungiyar tarayyar kasashen Turai, haka kuma kasashe da kungiyoyin kasa da kasa kimanin 50 ne suka tura wakilansu wajen taron.
Mr. Barroso ya bayyana cewa, an zartas da yarjejeniya kan sabbin manufofi game da Somalia, baya ga taimakon kudin Euro biliyan 1.8, an kuma yi kira ga kasar Somalia da ta dauki matakai wajen gudanar da shawarwarin siyasa, karfafa dokokin shari'a, kiyaye tsaron kasa da kuma bunkasa tattalin arziki da dai sauransu.
A nasa bangare, shugaban kasar Somalia Hassan Sheikh Mohamud ya bayyana cewa, wadannan kudade Euro biliyan 1.8 sun wadatar kwarai, hakan dai yana nuna niyyar gamayyar kasa da kasa ta inganta harkokin sake gina kasar ta Somalia. (Maryam)