Ministan ya ce, Saliyo ta kasance wani bangare na kasashen da ke bayar da gudummawar dakaru, kamar yadda yarjejeniyar kungiyar AU ta tanada, inda ya ce, wannan shi ne abin da kasar za ta saka wa Afirka da shi kan irin taimakon da ta baiwa Saliyo a lokacin yakin basarar da aka shafe shekaru goma ana yi a kasar, wanda aka kawo karshensa a shekarar 2002.
Conteh ya ce, abin da ya shafi daya daga cikin kasashen Afirka, hakika ya shafi sauran kasashen na Afirka, don haka ya ce, "idan har muka nade hannu muna kallon abin da ke faruwa a kasar Somaliya, to, tasirin hakan na iya shafar mu."
Ita dai kungiyar Al-Shabaab, reshen kungiyar Al-Qaeda ne da ke da mazauni a Somaliya, kuma Saliyo ta tura kimanin sojoji 800 da 'yan sanda 55 zuwa Somaliya, sannan nan ba da dadewa ba wani rukuni mai kunshe da 'yan sanda 150 zai tashi zuwa kasar ta Somaliya. (Ibrahim)