Mr. Wang wanda ya bayyana hakan bayan rattaba hannu da ya yi akan wata yarjejeniyar aiwatar da wannan aiki tare da firaministan Kasar Rui Duarte Barros, ya ce wannan agajin yana cikin taimakon da Sin ta yi niyyar baiwa kasar sakamakon bukatar hakan da ta nuna, dangane da yunwar dake barazanar kamar al'ummarta saboda karancin abinci, musammam ma a kauyukan karkara.
Sai dai jakadan bai bayyana adadi ko kwatancin nawa ne agaijn zai kama ba.(Fatimah Jibril)