in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi yunkurin juyin mulki da bai yi nasara ba a kasar Guinea-Bissau
2011-12-27 17:11:10 cri

A daren Litinin ne a yankin Afirka ta yamma, sojoji sun yi yunkurin juyin mulki da bai yi nasara ba a kasar Guinea-Bissau, a yanzu haka dai, mai jagorancin dakarun gwamnatin kasar Antonio Injai ya ce suna rike da madafan iko.

A kalla mutun guda ya rasa ransa a yayin da dama suka ji rauni a cikin kwashi ba dadin da ya wakana tun da safe a Bissau babban birnin kasar. Mutane kimanin 30 ne aka kama kamar yadda rediyon kasar ya sanar.

A yayin wani taron manema labarai, da ya samu halartar ministan ma'aikatar tsaro Baciro Dia da na ma'aikatar cikin gida Fernando Gomes , Janar Injai ya furta cewa wani gungun soji ne sun yi yunkurin juyin mulkin don kansu a ranar 26 ga watan Disamba, kan maganar zaman lafiya a cikin kasar. Komi ya daidaita a cikin hannun dakarun gwamnati da na friminista Gomes Junior, kamar yadda ya sanar.

Da yamma ne bindigogi suka yi ta kara tsakanin dakarun hafsan hafsoshi da kuma na dakarun rundunar mayakan ruwa da Bubo Americo Bubo Na Tchuto ya jagora.

Janar Injai ya sanar da cewa an dakatar da Bubo tare da abokin shi Sae Braia Na Nhakba da kuma wani babban jami'i mai sunan Watna Na Lai wanda ke karbar jiyya tare da Labtanal Tcham Na Man a asibitin Simao Mendes dake Bissau.

Ga dukkan alamu dakarun bangaren Bubo sun tsare hafsan hafsoshin kasar har zuwa karfe 5 na safe kafin ya samu taimako daga bangaren dakarun da suka zo daga Mansoa, wuri mai tazarar kilomita 50 daga arewacin Bissau, babban birnin kasar.

Bayan harbe-harbe, a garin na Bissau, tituna sun kasance babu kowa, babban gidan asibiti na Simao Mendes ya kasance a rufe yake inda sojojin tsaro ke sa ido a kai.

Wannan lamari ya wakana ne a daidai lokacin da shugaban kasar Malam Bacai Sanha ke samun jiyya a kasar Faransa. Mai shekaru 64 a duniya, shugaban ya je kasar Senegal makwabciyar kasar ta Guinea Bissau a watan da ya gabata kafin ya tafi kasar Faransa neman magani.

An dai zabi Sanha da ya zama shugaban kasar a shekara ta 2009 bayan kisan gillar da aka yi wa tsohon shugaban kasar Nino Vieira da kuma Janar Batista Tagm na Wai, a watan Maris na wannan shekara.

Kasar Guinea-Bissau da ta samu mulkin kai daga kasar Portugal a watan Satumba na shekara ta 1973 na fuskantar juyin mulki iri iri, tana da yawan mutane da ya kai miliyan 1.7 a halin yanzu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China