Yayin bikin da ya gabata a jiya Asabar, shugaban kungiyar tattalin arziki da masana'antu ta kasar Sin Li Yizhong ya bayyana cewa, kamfanonin da suka samu lambobin yabon, sun kai ga fidda wasu mahimman fasahohi a fannin kirkira, da ikon mallakar ilmi, matakin da ya sanya su, ciyar da kyautatuwar fasahohin gaba.
Har wa yau irin wadannan kamfanoni, a cewar Mr. Li sun daga matsayin aikin da kasar Sin ke yi a fannin raya masana'antu zuwa wani sabon matsayi, da kuma inganta kwarewar kasar Sin a wannan fanni tsakanin kasashen duniya.
Bugu da kari, Mr. Li ya bayyana cewa, kamata ya yi kasar Sin ta ci gaba da kyautata tsarin ayyukan masana'antu don bunkasa su, kamar batun kara samar da fasahohi na kashin kai, da zuba jari da dai sauransu. (Maryam)