Saurin karuwar tattalin arziki da manyan masana'antun kasar Sin suka samu ya kai kashi 9.3 cikin 100 a watan Afrilu na bana
Bisa alkaluman da hukumar kididdigar kasar Sin ta samu a ran 13 ga wata, an ce, a watan Afrilu na bana, yawan karuwar tattalin arziki da manyan masana'antun kasar Sin suka samu ya kai kashi 9.3 cikin 100 bisa na makamancin lokaci na bara, kuma saurin karuwarsa ya karu da kashi 0.4 cikin 100 bisa na watan da ya gabata.
A watan Afrilu na bana, sana'o'i 40 daga cikin manyan sana'o'in masana'antu 41 na kasar Sin sun samun karuwar kudi bisa na makamancin lokaci na bara.
Har ila yau a Afrilun, yawan kayayyakin da manyan masana'antun kasar Sin suka sayar ya kai kashi 98.5 cikin 100, abin da ya karu da kashi 0.4 cikin 100 bisa na makamancin lokaci na bara.(Bako)