in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na taka muhimmiyar rawa ga bunkasa masana'antu a Afrika
2013-04-18 11:08:42 cri

Gwamnatin kasar Sin da kamfanonin kasar Sin na taka muhimmiya rawa wajen samar da ayyukan yi da cigaban masana'antu a cikin kasashen Afrika, in ji wani jami'in diplomasiya na kasar Sin a lokacin da yake hira da wakilin kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua.

Da yake bayani a yayin dandalin harkoki tsakanin Sin da Afrika a birnin Johannesburg na kasar Afrika ta Kudu, mai ba da shawara kan harkokin tattalin arziki da kasuwanci na ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Afrika ta Kudu, mista Rong Yansong ya bayyana cewa, korafe korefe da ake na cewa, sanyen albarkatun ma'adinai da kasar Sin take ya yi daidai da mulkin mallaka ba su da tushe ko kadan.

Jami'in diplomasiya ya bayyana cewa, a fannin dangantakar kasuwanci, kasar Sin ba ta tilasta wa kasashen Afrika saye ko sayarwa kamar yadda kasashen yammacin duniya suka yi yau da shekaru 100, wannan ya sha bamban da yadda muke yi, wato yin ciniki bisa tushen daidaici da moriyar juna.

Kasashen Afrika na da albarkatun ma'adinai masu tarin yawa kuma mutanen kasashen Afrika na bukatar mai da wadannan albarkatu da Allah ya ba su a matsayin wata hanyar samun cigaba, game da haka ne kasar Sin take baiwa kasashen Afrika wannan babbar dama ta cimma burinsu.

Haka kuma manufar kasar Sin ba ta tsaya ga samun albarkatun ma'adinai a nahiyar Afrika ba, in ji mista Rong Yansong, kasar Sin tana amfani da taimakon da take baiwa kasashen waje domin gina hanyoyin mota, layin dogo, gada, makarantu, asibitoci a kasashen Afrika. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China