in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Akwai bukatar bangaren masana'antun nahiyar Afirka ya bayar da gudumawar kashi 25 cikin 100 na GDP din nahiyar
2013-06-11 16:55:08 cri

Wani jami'in MDD ya fada a ranar Litinin cewa, nahiyar Afirka tana da albarkatun da za ta iya fadada bangarenta na masana'antu, ta yadda zai bayar da gudummawar a kalla kashi 25 cikin 100 na GDP din nahiyar.

Darektar kungiyar raya masana'antu ta MDD (UNIDO) mai kula da shirye-shiryen shiyya na kungiyar Amita Misra ce ta bayyana hakan, tana mai cewa, a kalla a yanzu haka albarkatun nahiyar na bayar da gudummawar kasa da kashi 15 cikin 100 na GDP a sassa dabam-daban na nahiyar.

Misra ta fada a lokacin taron ministocin masana'antu na Afirka karo na 20 cewa, nahiyar tana da dukkan albarkatun da bangaren masana'antun ta ke bukata wanda zai samar da kashi 25 cikin 100 na GDP.

Taron na kwanaki biyar wanda kungiyar UNIDO da hukumar kungiyar AU da kuma gwamnatin Kenya suka shirya tare, wanda aka fara daga ranar 10 zuwa 14 ga watan Yuni, zai taimakawa nahiyar ta Afirka ta bunkasa dabarunta na masana'antu.

Misra ta ce, muddin nahiyar Afirka na son samun ci gaban tattalin arzikin da ake bukata, samar da guraben aikin yi da farfado da tattalin arzikin da zai kai ga rage talauci, wajibi ne ta samu a kalla kashi 25 cikin 100 na GDP da zai fito daga bangaren masana'antu.

Ta kuma ce kamata ya yi shiyyar ta bullo da sabbin matakan yin hadin gwiwa da kungiyar EU, kasashe masu karfin bunkasa tattalin arziki, da kuma kasashe masu tasowa domin a cike gibin da ke akwai.

Misra ta ce kungiyar UNIDO na aiki da sauran kungiyoyin raya tattalin arzikin Afirka da nufin bunkasa ayyukan da suka shafi masana'antu. Sannan akwai bukatar ita ma nahiyar, ta inganta kayayyakin da take samarwa ta yadda za su iya samun kafar yin gogayya a kasuwannin duniya. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China