Takardar kiyaye muhalli ta yi kira ga masa'antu da su kara mai da hankali game da kiyaye muhalli, da daukar alhakin da ke wuyansu wajen kiyaye muhalli, don cimma moriyar arziki da kiyaye muhalli tare, haka kuma, an yi kira ga masana'antu da suka je saka jari a kasashen waje da su bi dokokin wurin, kazalika ma, an bukaci ayyukan yin hadin kai wajen saka jari dake gudana a kasashen waje da suka samu izni daga hukumomin kula da harkokin kiyaye muhalli na wurin, su sauke nauyin da ke bisa wuyansu ta fannin kiyaye muhalli kamar yadda doka take bukata, haka kuma, an sa kaimi ga masana'antun da su yi nazari da koyi da ka'idoji da dokoki dake shafar kiyaye muhalli na kungiyoyin kasa da kasa da hukumomin hada-hadar kudi na kasashensu.
Ya zuwa karshen shekarar 2011, yawan masana'antun da Sin ta kafa a kasashen waje ya kai dubu 18, wadanda suke kasashe da yankuna 177, kuma yawan jarin da Sin ta saka kai tsaye ya kai kudin Amurka wato dalar biliyan 424.78. (Bako)