Bayan da aka samu raguwar saurin bunkasuwar masana'antu a farkon rabin shekarar bana, an fara samun karuwar hakan tun daga watan Yuli zuwa Satumba. Bisa kididdigar da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta yi, an ce, yawan GDP daga Yuli zuwa Satumba na kasar Sin ya karu da kashi 7.8 cikin kashi dari, wanda ya karu da kashi 0.2 cikin kashi dari bisa na farkon rabin shekarar bana. Kana yawan kudin da aka samu daga masana'antu a watanni 9 na farkon shekarar bana ya karu da kashi 9.6 cikin kashi dari bisa na makamancin lokacin bara.
Xiao Chunquan ya yi nazari cewa, an fara samun karuwar ce a madadin raguwa a fannin masana'antu, wannan ya bayyana cewa, ana samun bunkasuwa a bangaren masana'antun yadda ya kamata. (Zainab)