in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manyan masana'antun kasar Sin sun samu bunkasuwa sosai a watanni biyun da suka gabata.
2013-03-11 15:22:46 cri

Jaridar tattalin arziki ta kasar Sin ta ba da labari cewa, a cikin watanni biyun da suka gabata, manyan masana'antun kasar Sin sun samu bunkasuwa da karin kaso 9.9 cikin dari, bisa na makamancin lokaci na bara.

A watan Fabrairun da ya gabata an samu karuwar adadin da ya kai kashi 0.79 cikin dari bisa na watan Jarairu.

Haka nan yawan kayayyakin masana'antu da Sin ta sayar ya kai kashi 97.9 cikin dari, na dukkan kayayyaki da aka kera, wanda adadin shi ma ya samu karuwa da kashi 0.4 cikin dari, bisa na makamancin lokaci na bara.

Sai kuma yawan kudin da Sin ta samu a fannin fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, wanda yawan sa ya kai kudin Sin Yuan biliyan 1547, shi ma wannan adadi ya karu da kashi 7.8 cikin dari, idan an kwatanta shi da na bara war haka. Rahoton ya kara da cewa sana'o'i 40 daga cikin 41 sun samu karin bunkasuwa. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China