Mun yi imanin cewa, nagartattun matakan da aka dauka kan manufar ci gaban masana'antu cikin karko kuma bisa tushe za su hada da karfafa karfin sarrafawa ta hanyar da za ta dauki nauyin sauya gine ginen tattalin arziki, wadanda suka shafi karafafa bunkasuwar tattalin arziki, samar da nargatattun guraben aiki yi, kyautata aikin sarrafawa da cigaba, musanyar fasahohi da kimiyya da kuma karfafa bincike da cigaba, in ji wannan daftari.
A yayin da yake magana a lokacin bude babban taron, sakatare janar na MDD Ban Ki-moon ya tunatar da wannan duniya ta yanzu na fama da bambance bambance, sauye sauye da rashin tabbas. Mu ne ke shaidar ci gaban birane cikin sauri, wannan na nufin cewa al'umma na dadada karuwa, hakan na bukatar karin sarrafawa da ayyuka tare da raguwar albarkatun ma'adinai da rashin kulawa da datin masana'antu da gurbacewar muhalli. (Maman Ada)