in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aunin ayyukan cinikayya dangane da masana'antu da bana aikin hannu ba a kasar Sin a watan Afrilu ya samu bunkasuwa cikin daidaito
2013-05-03 16:23:29 cri

Kungiyar sufuri da sayen kayayyaki ta kasar Sin da kuma cibiyar nazarin sana'ar ba da hidimma ta hukumar kididdiga ta kasar Sin sun ba da labari a yau Jumma'a 3 ga wata cewa, a watan Afrilu, ma'aunin ayyukan cinikayya dangane da masana'antu da ba na aikin hannu ba ya kai kashi 54.5 cikin dari, wanda ya ragu da kashi 1.1 cikin dari bisa na watan da ya gabata, duk da haka, ya ci gaba da samu bunkasuwa cikin daidaito.

Tsarin ma'aunin PMI alkaluman sayan kayayyaki dake nuna ingancin tattalin arziki a bangaren masana'antu na ba na aikin hannu ba ya hada da ma'aunoni goma ciki hadda ma'aunin ayyukan kwangilolin, ma'aunin sabbin kwangiloli, ma'aunin sabbin kwangilolin kayayyaki da za a fitar da su zuwa kasashen waje da dai sauran su. Idan wadannan ma'aunonin ya haura kashi 50 bisa dari, ya nuna habakar wannan masana'antu ke nan, idan kuma bai kai wannan jimla ba, masana'antu ya samu koma baya. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China