Kasar Sin ta bayyana matakan da ta dauka don taimaka ma inganta masana'antu da za su kiyaye muhalli, su kuma kara yawan bukatu na gida, sannan a habaka tsarin tattalin arziki, kamar yadda wata sanarwa ta majalissar gudanarwar kasar ta fitar.
Kasar Sin da ta sha alwashi a cikin wani tsarin cigaba da ta fitar a bara cewa, za ta daga rage gurbatar muhalli da masana'antunta ke yi ta hanyar kara yawan haraji ga wanda ya gaza cimma tsarin daga RMB 4.5 triliyan kwatankwacin dalar Amurka biliyan 729.7 nan da shekarar 2015 ko kuma a kalla kashi 15 a cikin 100.
Majalissar kasar ta jaddada wannan buri nata a cikin bayanin da ta fitar na baya bayan nan, tana mai shan alwashin bullo da sabbin dabaru na fasaha, fadada ayyukan samar da ababen da ba na gurbata muhalli ba, tsimin makamashi da inganta ayyukan masana'antu da suka jibinci kiyaye muhalli.
Kasar Sin dai za ta ba da kwarin gwiwwa ga masana'antu domin su yi ayyuka a kasashen waje da suka shafi kare muhalli, haka zalika su ma masana'antun kasashen waje da suke nan za'a mara masu baya musamman ta wannan bangaren, in ji bayanin majalissar gudanarwar kasar. (Fatimah)