Kigbu, wanda ya bayyana hakan cikin sakon da daraktan tsare-tare, da kididdiga na ma'aikatar ya karanta a madadinsa, yayin bikin bude taro na 23 na Ranar Bunkasa Masana'antun Nahiyar da aka gudanar a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, ya kara da cewa wannan taro wata dama ce ga mahalartansa, ta hada karfi da karfe wajen tunkarar matsaloli, da kalubalen da sashen masana'antun nahiyar ke fuskanta.
Babban sakataren ya kuma bayyana irin gudummawar da masana'antu ke baiwa ci gaban al'umma, ciki hadda batun samar da ayyukan yi, da bunkasa tattalin arziki. Ya ce har yanzu Najeriya, da ma nahiyar Afirka, ba su ci cikakkiyar gajiyar dinbin al'ummar dake akwai a nahiyar ba, duk da mai da hankali da ake yi ga sassan tattalin arziki masu alaka da albarkatun mai da iskar gas a kasashe da dama dake nahiyar.
Bisa la'akari da hakan, Kigbu ke ganin lokaci ya yi da za a dauki dukkanin matakan da suka wajaba, don fadada cin gajiyar ragowar sassan tattalin arziki, da zasu amfani nahiyar ta Afirka. (Saminu Alhassan)