Shugaba Jonathan wanda ya bayyana hakan yayin wani bikin kaddamar da kwamitin kula da harkokin bincike da kirkire-kirkire na kasar a kwanan baya, ya kara da cewa kwalliya ba zata biya kudin sabulu ba, muddin kasashen Afrika suka ci gaba da dogaro kan kananan kayan da ake sarrafawa, da kuma danyun kaya wajen neman bunkasuwa.
Yace kamata yayi a zabi wata hanyar raya masana'antu da za ta inganta hada hadar kayayyakin cinikayya, da kuma samar da guraban aikin yi. Jonathan ya ce dole ne a canza yanayin da ake ciki a Najreiya, da ma nahiyar ta Afrika baki daya.
Sabon kwamitin da aka kafa dai zai kasance jigon tsara manufofin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha a kasar, wanda kuma shugaban kasar zai jagoranta, baya ga wasu ministocin kasar da zasu kasance mambobin sa. (Bilkisu)